Akalla mutum 21 ne jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar sun rasa rayukansu a wani sabon harin da yan bindiga suka kai jiya a wasu kauyuka guda biyar dake yankin kaduna ta kudu.

An fara kai harin farko ne a wani kauye dake karamar hukumar jama’a da yammacin ranar lahadi inda daga bisani kuma aka kara kai wani mummunan hari a wasu kauyuka guda uku dake karamar hukumar kaura da yammacin jiya litinin.

Kauyukan da harin ya shafa sune Ashim, Nissi da kuma Zilan dake karamar hukumar Kaura inda maharan suka kashe mutum 15 tare da kona akalla gidaje 50. Sai kuma kauyukan Bakin Kogi da kuma Kaninkon dake karamar hukumar jama’a inda yan bindigar suka kashe mutum bakwai.

Wani mazaunin yankin mai suna Enoch Barau ya shaidawa manema labarai cewa maharan sanye suke da bakaken kaya kuma dauke suke da manyan makamai, inda suka yi tayin harbin kan mai uwa da wabi a yayin da suka tunkaro kauyukan. Ya kara da cewar maharan sun shammaci lokacin da sojojin dake gadin yankunan ne kafin su kai harin..

Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da harin ta bakin mai magana da yawun gwamna a kafar sadarwar Samuel Aruwan, inda ya ce za’a kara daukar tsauraran matakai don kare aukuwar hakan nan gaba.