Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywwod Saima Muhammad ta fito ta shaidawa da duniya a wani irin salo na maida martani da babbar murya cewar su ma fa ‘ya ‘yane kamar dukkan sauran mata.

Jarumar tayi wannan kalaman ne a yayin wani taron da fitattun matan fim din suka shirya da zummar kafa kungiyar su a wani dakin taro dake a cikin garin Kano.

Saima Muhammad dake jagorantar tafiyar ta kungiyar ta fada a cikin jawabin nata cewa makasudin kafa wannan kungiyar tasu shine domin fadakar da al’umma irin darajar da matan fim suke da ita kamar sauran mata.

A cewar ta: “Mu ma mata ne masu daraja da kima tamkar wadan da iyayen su ke killace su ko kuma su kaisu kasashen waje yin karatu.”

Ta cigaba da ciwa daga cikin manufofin kungiyar ta su za su rika kai ziyara asibiti tare kuma da taimakwa marasa lafiya da sauran marasa galihu a cikin al’umma.

NAIJ HAUSA