an sace dauda kahutu rarara

Shahararren mawakin Hausa kuma shaharrare a wakar siyasa wato Dauda Adamu Abdullah Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya bayyana yanda wasu masu garkuwa da mutane suka sace shi gami da karban kudi har naira milliyan biyu da dubu dari takwas a gurinsa (2.8million) kafin su sake shi.

A hirarsa da yayi da jaridar Dailytrust ta yau lahadi, mawakin ya bayyana yadda lamarin ya auku a ranar alhamis din nan data gabata. Ya bayyana cewa mutane sun bishi har gidanshi dake Zoo road a ranar alhamis inda sukayi awon gaba dashi.

“Na dawo da misalin karfe daya na dare (1am) ina kokarin shiga gida kawai sai naga wasu mutum hudu a gabana, inda daya daga cikinsu ya tsinkamin mari, kafin daga bisani suka turani cikin motata sannan suka tafi dani.”

Ya kara da cewa bayan sun dauke shi sai sukayi wajen tudun fulani dashi, bayannan kuma sai suka nutsa cikin gari suka yi yan kewaye kewaye na tsawon kamar minti talatin (30) kafin daga bisani suka tsaya, sannan suke shaida mashi cewa an turo su ne su kashe shi, amma idan yana da kudi da zai basu to shikenan.

Rarara ya bayyana cewa ya basu duka kudin dake tare dashi wato milliyan biyu da dubu dari takwas. Sannan sai mutanen suka umarce shi da ya tube kayansa sannan kuma ya kwanta a kasa kafin daga bisani suka gudu da kudin da kuma motarsa..

Sai dai mawakin ya bayyana cewa ba mamaki a cikinsu akwai wanda ya sanshi sosai tunda ya lura da daya daga cikinsu yana ta noke murya dan baiso indo muryar sa..

Da farko dai yayi zaton cewa ko jami’an tsaro ne, amma daga baya sai ya fahimci cewa ba jami’an tsaro bane. Rarara din ya mika rahoto ga jam’an tsaro dangane da faruwar lamarin, sannan yayi kira ga masoyansa da su tamashi da addua..

To jama’a, abinda mukeji na garkuwa da mutane a can nesa, yankin wasu kabilun sai gashi yau yana nema ya zama ruwan dare anan yankinmu na arewa, koma dai menene, Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu…