Wata mata da wasu mutane da ake zargin yan bokoharam ne suka sace a maiduguri sannan suka yi yunkurin daura mata bomb domin ta tashe shi a kasuwar kantin-kwari Kano ta kubuce daga hannunsu.

Kakakin yan sandan jihar Kano wato Abbati Maigari Dikko ne ya bayyana hakan bayan gabatar da ita wannan mata a gaban mai girma gwamnan jihar Kano.

Ita dai wannan mata mai suna khadija Ibrahim ta bayyana cewa yayin data fito bakin titi ne don ta tari motar da zata hau domin ta kaita zuwa asibiti inda a nan ta shiga cikin motar su mutanen da bata san ko su waye ba.

Matar ta kara da cewa shigarta ke da wuya cikin wannan mota sai kawai tarasa inda kanta yake ba na tsawon lokaci. Farkowar ta ke da wuya sai jinsu tayi suna labarin yadda zasu kaita kasuwar kanti kwari domin su tayar da bomb da ita.

Khadjia tace bayan ta duba jikinta ne sai ta fahimci cewar har sun daura mata belt din bomb na kunar bakin wake, amma cikin ikon Allah sai motar su ta samu matsala inda cikin wannan haline Allah ya bata sa’ar kubucewa daga hannunsu.

Allah ya kara kiyaye mu, ya kara dawwamar mana da zaman lafiya a Nigeria……