Jama’a barkanku da warhaka, deendabai ne ke muku marhabun da wannan lokaci na safiyar ranar laraba.

A wasu lokutan wasu sukan sanya wa wayoyin su na android tsaro don gudun kada wani ya shiga ya ga wani abun da ba sa so wani ya gani ko kuma wani abu na sirri ko kuma gudun kada wani ya shiga yayi maka barna da dai sauran makamantan irin wadannan dalilan.

Idan abun yazo da matsala sai kaga ka manta pattern,pin ko kuma password da ka sanya. Wasu lokutan kuma kana da yakinin cewa abunda kasa dai dai ne amma dukda haka sai taki budewa wanda hakan zai tilasta ma ka yin flashing na wayar wanda daga karshe hakan zai haddasa maka rasa wasu files naka dake kan wayar irinsu apps, pics, docs, videos, contacts dadai sauran makamantansu.

A yau cikin ikon Allah da yardar sa zan yi muku bayani kan yadda mutum zai cire/balle pattern , pin ko password ba tare da ya rasa ko daya daga cikin apps dinsa dake kan waya ba.

Abubuwan da ake bukata


– Wayar da ake son cirewa tsaron
– Aroma File Manager (Dauko shi daga Nan
– Memory card da za’a ajiye aroma FM din a cikin.

Matakan da zaka bi

Da farko dai sai ka kwafi shi wannan Aroma file manager.zip zuwa cikin memory card din da zakayi amfani dashi sannan sai ka sanya shi a cikin wayar da kake son budewa din..

Sai ka cire SIM card dinka daga cikin wayar (in case of matsaloli daka iya biyo baya) sannan ka kashe wayar.

Bayannan sai ka shiga recovery mode din wayarka, ya danganta ga irin wayar da kake amfani da ita, amma dai yawancin wayoyi suna amfani da power da kuma volume key ne.. So a yayin da wayarka take a kashe sai ka danne abin kunnawa(power key) tare da abin rage volume (volume down) a tare sannan ka danne su zuwa kamar tsawon dakika 15(15seconds) inda zaka ga ta kawo maka wasu abubuwa kamar guda 5 zuwa 7

Daga nan sai kayi amfani da volume down wajen sauka zuwa kan abubuwan da ake da bukata. So sai ka sauko kan Mounts and storage sai ka dannan power ke domin shiga ciki,idan yaki to sai ka dannan volume up.

Daga nan sai ka zabi wadannan ; “mount /system” sannan sai “mount /data” sannan sai “mount /efs” sannan sai “mount /preload” sannan “mount /sdcard” sannan “mount /external_sd”.. Sai kaje can kasa ka zabi Go back

Mataki na gaba shine wanda zamuyi install na aroma file manager app da muka dauko abaya.. So sai ka shiga install zip from sdcard sannan sai ka shiga Choose zip from sdcard sai ka nemo shi sannan ka zabe shi inda zaka ga an rubuto maka “Yes Install Aroma File Manager” sai ka zabi wannan sannan ka jira ya gama. Daga ya gama zaka ga ya bude maka app din.

Sai ka shiga wajen setting sannan ka zabi Automount all device on start daga nan sai ka fita daga cikin app din , so kaga zaka kara komawa recovery mode inda zaka kara install din aroma file manager kamar yadda kayi a baya amma wannan karon zai bude abubuwa da yawa.

Zaka ga ya kawo maka abubuwa inda daga ciki zaka ga wata folder mai suna Data so sai ka shiga, daga nan kuma sai ka shiga system sannan ka nemo gesture.key in ya kasance da da pattern aka kulle ta ko kuma password.key in ya kasance da password aka kulle ta.. Bayan ka gano gesture.key ko kuma password.key din kawai sai ka danne shi zaka ga ya nuno maka delete sai kawai ka goge. Da zarar ka goge sai ka fita daga application din sannan ka kashe wayar sai ka kunna ta. Zaka ga an nuno maka kasa pattern, to sai kawai kasa sabon pattern da kake so wanda ba zaka manta ba. Haka zalika in password aka tambayeka to sai kasa wanda ba zaka manta ba.

Zaka iya amfani da gmail din dake kan wayar ka wajen dawo balle kwadon dake kai ta hanyar shiga link din forgot pattern ko password

Idan ya kasance duk matakan dana zayyana a sama ba suyi maka aiki ba, to lallai babu makawa kayi wiping na wayar baki daya..

Yadda zaka yi wiping din wayar baki daya

Wannan matakin zai goge dukkanin wani abu dake kan wayar ka, ma’ana zata koma sabuwa kamar yadda aka yota daga kamfaninta.

– Da farko dai sai ka kashe wayar sannan ka cire SIM card dinka da memory card.

– Sai ka matse malatsin rage volume da kuma malatsin kunnawa na kamar tsawon dakika 15(15secs).

– Zaka ga list din zabuka da yawa, ba mamaki kaga harda rubutum Chinese ma, to sai ka lura dakyau zaka ga inda akasa clear eMMc ko kuma factory reset / wipe data.. Sai ka shiga ta hanyar amfani da makunnin wayarka ko kuma abun karo kara…

Ina fatan wannan dan takaitaccen bayani nawa ya kayatar…