Jama’a barkanku da wannan lokaci. Deendabai ne ke muku lale marhabun da zuwa shafin mu mai albarka na arewamobile wanda ako da yaushe yake kokarin kawo wa al’umma bayanai kan abubuwa na cigaban zamani, inda a wani lokacin kuma mukan kawo bayanai kan yadda za’a warware wasu matsaloli dake damunku akan amfani da wayoyinku na hannu.

Darasin mu na yau cikin ikon Allah zai yi muku bayani ne akan yadda mutum zai dauki hoton video din wasu abubuwa da yake aiwatarwa akan wayarsa ta android. Misali zaka iya yin video recording na game a yayin da kake bugata, zaku ma ka iya yin video recording din yadda ake amfani da wani app ko kuma wani setting don ka turama wani abokinka ya ga yadda ake yi da dai sauran wasu abubuwan masu amfani.

Ba tare da bata lokaci ba, zamu tsunduma cikin bayanan mataki daya bayan daya, kama daga app da ake bukata zuwa ga yanayi ko kuma irin wayar da ake bukata.

Abubuwan da ake bukata
Domin ka samu damar aiwatar da screen recording akan wayarka to sai ya kasance kana da wadannan abubuwan:

• AZ Screen recorder (wanda zaka iya samunsa a playstore ko kuma ka dauko shi daga nan link din

• Ya kasance wayarka tana running din akalla lollipop 5.0 ko fiye da haka (kenan idan wayarka 4.4.2 ce sai kayi upgrade dinta zuwa 5.0 so sai ku tuntubi abokina Sadik nasir a.k.a sadik developer )

Idan ya kasance ka cika sharuddan dana zayyano a sama to sai ka cigaba da binna sannu a hankali don fara aikin wanda zan fara zayyano matakan kamar haka:

• Da farko dai sai ka bude shi wannan app daka dauko (wato az screen recorder) sannan sai ka danna wajen alamar setting dake can sama inda ze kaika wajen da zaka wasu rubuce-rubuce to sai ka zabi resolution sannan ka saita shi zuwa Full HD 1920×1080 ko kuma resolution din da kaga dama.

• Bayanan zaka ga Frame rate sai ka maida shi zuwa 30 FPS

• Sai ka sauka kasa can wajen Record audio don ka tabbatar da cewa a kunne yake saboda yayin da kake video recording din to duk maganar da kake yi ma duk za’a dauka.

• Sai wajen Show touches shima ka tabbata yana kune domin wanda ka tura wa video din yaga abinda kake tabawa.

Daga ka gama wadannan saite-saitan sai ka fita ka koma baya, daga sama zaka ga wani jan icon to sai ka tabashi, da zarar ya gama kirga wadannan seconds din to shikenan zai fara recording din duk wani abu da kake yi akan wayar taka, ya’alla game ce ko kuma kana sarrafa wani application din ne. Haka zalika duk maganar da kayi ita ma za’ayi recording dinta tare da video din.

Idan kana so ka tsaya ko kuma in ya kasance ka gama kuma kana so ka tsaya da video recording din hakanan, to sai kawai ka jawo saman wayarka inda zaka ga STOP sai kawai ka taba shi, take app din zai tsaya da recording sannan kuma ya ajiye maka video din a Mp4 a kan wayarka cikin folder mai suna AZRecorderFree ko kuma kawai ka duba cikin gallery inda zaka sameshi cikin videos dake gun.

Dukda cewa akwai video editing tabs a cikin application din, ba zasu isheka ba in ya kasance kana son kadan yi gyare-gyare ko kuma kare-kare a cikin video din. Saboda da haka kana iya dauko wani video editor din a playstore in ya kasance zaka bukaci hakan.

Shawara:
Idan bakason hayanayi da yawa ta shiga cikin recording to sai kayi amfani da earpiece yayin da kake screen recording din.

Ina fata wannan dan takaitaccen bayani da nayi ya ilmantar, fadakar sannan kuma ya gamsar. In akwai wanda bai gane ba ko kuma yake bukatar karin bayani to sai yayi comment da bukatar shi ko kuma ya neme ni ta facebook Deen Dabai ko kuma ya tuntube ni ta lambar waya 08135658217

Ku tura ma abokanenku da ke Facebook , Twitter , Whatsapp da sauransu ta hanyar latsa share buttons dake kasa..