Jama’a barkanku da wannan lokaci, deendabai ne ke muku marhabun da kasancewa da mu a cikin wannan darasi mai matukar amfani wanda zai yi bayani kan yadda zaka yi tracking din ainihin gurin da mutum yake ta hanyar amfani da wasi fasahohi.

Ya kan kasance kana chat da mutum batare da ka san ko waye shi ba kuma baka san ainihin daga inda yake ba. A wasu lokutan kuma wani ka iya yi maka karyar cewa yana wani gurin alhalin ba haka zancen yake ba. To a yau in sha Allahu zan tsage maku bayani kan yadda zaka ga ainihin “location” da mutum yake.

Zamu yi amfani da chat da aka fi yi a yanzu wato Facebook chat. Inda zamu yi amfani da ip(internet protocol) address na mutumin da kake chat dashi wajen gano ainihin gurin da yake a yayin da kuke chat din.

Akwai hanyoyi da dama da za’a iya tracking (bin diddiki) din mutum a harkar yanar gizo-gizo, zamu zayyano muku wasu daga cikin wadannan hanyoyi a nan kasa.

Ta amfani da command prompt

Da farko dai dole ka dakatar da duk wani abu da kake akan computer dinka baya ga chat din da kake yi a wannan lokaci.

Sai ka dannan Win tare da R (Win+R) daga nan zaka ga ta kaika wajen wani page daban dauke da akwatin rubutu sai kawai ka rubuta cmd sannan ka danna Enter.

Da zarar ka danna Enter to za’a kaika zuwa cikin command prompt app , sai kawai ka rubuta netstat -an sannan ka danna Enter . zaka ga wasu rubuce-rubuce da yawa daga ciki zaka ga IP address din wanda kake nema misali 123.096.454.001 sai kawai ka kwafe shi sannan sai kaje wannan website din http://whatismyipaddress.com/ip-lookup inda zaka ga wani akwatin rubutu sai kai paste din ip din sannan ka danna ok akan Lookup IP Address ..

Da zarar kayi hakan to page din zai yi loading idan ya gama kuma zai kawo maka bayanan network da me ip din ke amfani dashi, suna browser , sunan gari, unguwa, kasa sannan kuma zai hado maka da map din inda me ip din yake.

Akwai hanyoyi da dama da za’a iya bi don samun ip address na mutum gami da nemo ainihin inda yake.

Tura wa abokai..