Barkanku da warhaka maziyarta shafinmu mai albarka na arewamobile , shafin da a koda yaushe yake kokarin kawo muku bayanai kan abubuwa da suka shafi wayoyin hannu inda a wasu lokutan mukan dan taba fannin na’urar kwamfuta da sauran ababe da suka shafi fasahohin zamani.

A yau cikin ikon Allah zamu kawo muku bayanai akan matakan da zaku bi don ku mayar da wayoyinku na android zuwa tsarin android 7 ko wanda aka fi sani da Nougat wacce take a mazaunin manhaja mafi girma a kira android.

Android Nougat (Android 7) itace sabuwar manhaja kuma babba a tsarin zubi(version) na wayoyin android. Akwai wasu zube-zube na wayar da dama; kama daga kitkat 4.2.2 , lollipop 5.0.1 , marsmallow 6. , ya zuwa kan android 7 (Nougat).

Ba dole bane sai mutum ya kasance yana siyan duk irin wayoyin dake dauke da wadannan zube-zuben bane zai iya samun damar more su ba. Mutum zai iya more su ta hanyar bunkasa (update) wayar tashi zuwa duk irin sabuwar manhaja wacce ke dauke da zubin da yake so muddun kamfanin wayar tashi ya bashi damar yin hakan ko kuma ta hanyar yin amfani da kwanfuta. Sai dai ba kowacce waya bace ke samun wannan dama inda a dalilin hakane na yanke shawarar yin rubutu kan yadda zaka mayar da wayarka zuwa kamannin android Nougat din.

Matakan Da Za a bi

Ba tare da wani dogon surutu ba, wasu apps ne kawai zaka dauko sannan kayi install dinsu akan wayarka. Ga applications/softwares da ake bukata:

– Nougat Launcher :- Launcher ce da zata mayar da hotuna da kuma icons na apps din wayarka su koma kamar na android.

– N Dialer+Calci :- Application ne da zai mayar da dialpad din kira da na calculator din wayarka zuwa irin na Nougat.

Ragowar apps din ake bukata sune: Android N-ify the status bar , Twilight , Xposed Installer da sauransu..

Duka apps din dan zayyano a sama suna nan a playstore, so sai a shiga playstore domin sauko dasu kan wayar

Ina fata da wannan dan rubutu nawa wasu zasu amfana wajen kawata wayoyinsu don jin dadin amfani dasu. Ba daidai bane ka yiwa wani ko wata karyar cewa wayarka version 7 ce, alhalin kana rike da kitkat ne…..

Tura wa abokai…