Jama’a barkanku da warhaka, Deendabai ne ke muku lale marhabun da zuwa shafinmu mai albarka na arewamobile.

A kwanakin baya dai in ba a manta ba Ahmad Yusuf yayi rubutu a kan Yanda zaka more N975 akan N90 kacal a MTN wanda hakan dama ce kadai ga Wadanda ke tsarin kira na MTN zone.

Nasan akwai da yawa daga cikin masu karanta wannan rubutun da suka dade da sanin wannan dubarar, saboda haka wannan rubutun anyi shi ne ga wadanda ba su san da wannan hikimar ba.

Ba tare da wani dogon surutu ba bari in fayyace muku yadda abun yake baki daya.

-Da farko dai dole ne ka kasance mai amfani da MTN V300(in baka san yadda tsarin yake ba to shiga nan ka karanta.

-Ya kasance account balance naka 0.00 yake(ka cinye bundle bonus din da kuma kudinka na waya baki daya)

Idan ka cimma matakan da ke sama, sai kawai ka sanya katin N100 sannan sai kawai ka kira lambar da kake son kira ja ci gaba da magana ba tare da ka yanke ba har zuwa lokacin da kaji ka gamsu da kiran wayar. A wannan kira na farko zasu rinka chajin ka akan 0.12kb per second wato N7.2 per minute. So idan ka auna zaka ga cewar wannan bonus na N975 da suka baka zai yi minti 135.41 kana kira in baka yanke kiran ba.

Amma fa kada a manta da cewar a kiran farko ne kawai zai kasance ana chajinka akan N7.2 a duk minti, saboda haka a kira na biyu zasu cigaba da daukar N24 kamar yadda yake a tsarin…..

Wannan shine gaba daya bayanin yadda zaka more wannan garabasa ta tsawon kira akan kudi kalilan.

Sai dai hakan zaifi amfani ne ga wadanda suke da wani kira mai tsawo da zasu yi(ba mamaki hira da budurwarka ko saurayinki)….

Tura wa abokai…