Deen Dabai ke muku barka da wannan lokaci. A can baya ne kamfanonin layukan wayoyi a Nigeria suka fiddo da tsaruka na saukin kira da kuma na saukin data ta browsing. Cikin wadannan kamfanonin layukan kuwa harda layin airtel wanda suka fiddo da tsarin browsing na dare akan farashi mai rahusa.

A yau airtel sun kara fito da wani sabon tsarin da yafi na can da sauki tunda shi zai baka damar samun 1.5GB akan N50 da kuma 500MB akan N25 wanda dukkansu zasu fara aiki daga 12am har zuwa 5am na asubah, Sabanin wancan na da da ya kasance yana aiki a awa 1 ne kawai..

Domin more wannan garabasar data sai ka biyoni sannu a hankali cikin bayani na.

Da farko sai ka canja tsarin layinka zuwa airtel smart tribe plan. Smart tribe ya kasance tsari mai sauki ko kuma ince tsari mafi saukin kira a Airtel domin suna cire kwabo 11 ne duk sakan(11k/sec) zuwa kowanne network kaga kenan N6.6 a duk minti kenan.

Yanda zaka koma smart tribe ba wani abu bane mai wahala face kawai ka dana *312# sai ka kira, zaka ga na 1 migrate sai ka shiga.

Domin siyen data kuma, sai ka danna *312*3# sannan ka kira, zaka ga an baka zabuka guda biyu; na farko 500MB akan N25, sai na biyu 1.5GB akan N50 sai ka zabi wanda ya kwanta maka a rai..

Inda har kamfanin airtel suka dore da iren wadannan ofofi, to tabbas zasuyi zarra sosai.

DEEN DABAI
WWW.AREWAMOBILE.COM