A har kullum ana kara samun cigaba a fannin fasahohin zamani musamman wadanda suka shafi na wayoyin hannu da kuma na’ura mai kwakwalwa ta yanda ake kara inganta manhajojin su da sabbin sauye-sauye don jin dadin masu amfani da su a koda yaushe. Mutum yakan sami damar yin abubuwa da dama da wayarsa ta hannu wadanda da sai dai a na’ura mai ake iya yin su musamman in akazo bangaren abubuwan da suka shafi yanar gizo, manhajojin bincike-bincike, tsaro zuwa bangaren gyaran hotuna, zane-zane da sauran abubuwa da dama.

Akwai matukar cin rai ace sai bayan da ka cika wayarka da manhajoji, hotuna, litattafai, bayan masu muhimmanci da kuma wasu bayanan na sirri kwatsam sai wayarka ta bace ta hanyar faduwa ko kuma ya kasance an sace ta wanda hakan ke nuni da cewar wani zai shiga ya ga duka wasu bayanai naka na sirri da sauran wasu abubuwa muhimmai a gareka. Domin rage radadin zafin da hakan zai jawo maka ne yasa shafin arewamobile.com yayi kokarin binciko muku hanya mafi sauki da zaka bi don yin rigakafi a kan wani ya samu damar iya ganin bayanan kan wayarka a yayin data bata, ku kasance tare dani Deendabai don samun cikakken bayani daga farko har karshe, amma kafin nan, sai mu dan sha ruwan zafi da coffee kadan..

Akwai manhajoji (apps) da yawa da akanyi amfani da su wajen goge(wiping) ko kuma formatting din waya a yayin data bata ko kuma ta fadi, daga ciki akwai irinsu Android Device Manager na google wanda kan baka damar ganin ainihin gurin da wayar ka data bata take, sannan kuma ya baka damar kulle wayar da makullen sirri(pasword) ko kuma baka damar goge duka abubuwan dake kan wayar muddun dai zaka iya amfani da google account
dinka dake can kan wayar.

Android Device Manager da sauran manhajoji da kanyi ayyuka irin nasa na da nakasu guda daya zuwa biyu;akwai bukatar sabis din yanar gizo(Internet connection) ko kuma bukatar tura sako ta sms wadanda sun dogara ne ga kasancewar data a bude ko kuma kasantuwar layin wayarka a ciki, kaga kenan da an cire layin naka an yar shikenan, wanda hakan ke nuni da rashin tabbacin samun nasarar goge bayanan kan wayar taka data bace..

Duba da irin matsalolin dana zayyano muku a sama yasa nayi kokarin binciko muku wata hanyar da za’a iya bi wajen kaiwa ga ci kuma alhamdulillahi, don yanzu haka na samo muku bayani kan wani application mai suna Erado wanda baya bukatar data ko kuma kasantuwar layin ka a ciki.

Menene Erado kuma ya ake amfani dashi?

Erado wata manhaja dake baka damar saita wayarka ta yanda zaka iya goge kayan dake cikinta a yayin da ta fadi daga hannunka. Wannan manhaja ta kunshi tsaruka guda biyu wato tsarin kyauta da kuma na kudi(pro version) wanda duka kowanne yana aiki yadda ya kamata.

Da farko dai sai kaje playstore ka dauko wannan manhaja ko kuma ka bi ta wannan adireshin Erado – playstore

Bayan ka dauko shi sai ka kafa shi akan wayar taka ma’ana sai kayi install dinsa sannan sai ka bude shi inda zaka ga wani akwatin sako dauke da rubuce-rubuce sai kawai ka danna close.

Daga zaka ga hoton makunni ya fito a tsakiya sai kawai ka danna shi inda zai tambayeka izinin yin wasu abubuwa akan wayarka duk sai ka bashi dama

Da zarar ya gama wannan to sai mu auka zuwa ainihin inda zamu saita yadda muke so abin ya kasance.

Domin shiga cikin satukan app di sai ka jayo screen din zuwa barin hagu inda zaka samu kanka cikin shafin saituka na wannan manhajar wanda daga nan ne zaka iya saita lambobin password da kake son yin amfani da.

Zaka ga gurin da aka rubuta Triggers ma’ana musabbabai, wanda kasan rubutun zaka ga zabukan abubuwan da in aka yi daya daga cikin su zai tsokalo gami da ba manhajar Erado kaddamar da aikinta. Daga ciki akwai :

Receiving sms – ma’ana aba Erado damar daukar mataki ta hanyar tura sakon password din daka saita zuwa layinka dake kan wayar data bace din.

Akwai Sim card removal – wannan saiti ne dake kunna Erado da zarar wanda ya dauki wayar ya cire Layinka daga cikin wayar

Akwai Blocked Simcard, Simcard replacement da sauransu kamar yadda zaku iya gani a hoton nan dake kasa.

Daga cikin matakan da wannan manhaja zata iya dauka akwai; turo maka lambar layin da aka sa a cikin wayar taka da aka dauka da kuma goge duka kayan kan wayar wato format ko wiping na kayan kan wayar ko kuma ta goge duka lambobin dake cikin SIM card ko kan wayar taka. Sai dai kuma akwai hadari akan hakan duba da cewar wataran zaka iya mancewa ka cire layin daga wayar taka ba tare da ka tuna da cewar cire layi na cikin abubuwan dake kunna wannan manhaja taka ba. Ina ganin saitin da zai turo maka lambar wanda ya dauki wayar taka zaifi.

Abin lura: Yana da kyau ga duk wanda zai aiki da wannan manhaja to ya kasance yayi taka tsan-tsan wajen saurin cire layinsa daga wayarsa don gudun matsala. Kada kazo daga baya kana cewa Deendabai ya ja maka goge kayan kan wayarka masu amfani.

Ku tura ma abokanenku dake shafukan sadarwa na zamani don suma su karu.

Marubuci: Deendabai
arewamobile.com