Jama’a barkanku da wannan lokaci, Deendabai ne ke muku lale marhabun da zuwa shafi mai albarka wato shafin arewamobile, wanda ako da yaushe ke kokarin kawo ma masu ziyartarsa bayanai masu matukar amfani musamman bayanai da suka shafi matsalolin waya da maganinsu.

To yau ma dai kamar yadda aka saba muna dauke da wani darasi da zai muku bayani kan yadda mutum zaiyi “cloning” ma’ana Yanda zai kwafi ko kuma matsar da duk abubuwan dake cikin tsohuwar wayarshi ta android zuwa sabuwa ba tare da ya tsaya backup ko wani abunba.

Nasan da yawa zasu ce ai ga backup nan, banki ta taku ba amma idan ya kasance babu isashshen guri akan wayarka ko kan memory card dinka fa ya zakayi kenan?

Kuma Sannan ka sani ita wannan hanyar zata baka damar kwashe komai da komai har settings, apps,contacts,accounts, launchers dadai sauransu.

Ba tare da na cika ku da dogon labari ba, zan zayyano muku matakan da zaku bi daya bayan daya don cimma wannan aiki.

• Da farko dai ya kasance kana application na android da ake kira da CLONEtwiakan duka wayoyi biyun. Idan babu app din akan wayarka to sai ka dauko shi
Daga nan .

• Bayan ka sanya wannan application din a duka wayoyin sai ka bude shi zaka ga ya baka zabuka guda biyu wato Sender da kuma Receiver sai ka zabi sender a wayar da za ka tura sannan sai ka zabi receiver kamar yadda yake a hoton nan

Bayan nan zaka tayi search kamar Yanda Xender keyi sai kai connect dinsu, daga nan zaka list din duka abubuwan dake wayar sai ka cigaba da turawa, kamar yanda yake a hoton nan

Waddan sune bayanai kan matakan da zaka bi don cloning din kayan wata wayar zuwa wata.

Ku tura ma abokanku dake Facebook, Twitter , Whatsapp da sauransu.