whatsapp-video-call

Shahararren kamfanin sadarwar nan na whatsapp na shirin sanya tsarin yin kira ta hanyar amfani da camera dake jikin fuskar wayarka wato video call kamar irin na skype, facetime da sauran makamantansu.

Idan baku mance ba a chan baya kamfanin whatsapp wanda yake mallaki ne na kamfanin Facebook ya kara sanyo wasu sabbin abubawa da suka hada da bada damar yin kira wato voice calling, damar tura pdf files, kara yawan members da group ke dauka, cire charging kudi da ake na $1, da kuma karo tsaron sirrin sadarwa (end-end encryption) da sauransu..


Photo:Phoneradar

Bayanai a yanzu sun tabbatar da cewa kamfanin na nan na shirin sanya tsarin kira na photo mai motsi wato video calling a sabon version da su saki nan gaba, wato a version 2.16.3.525.

wayoyin da zasu more wannan canji

kasantuwar iPhone da kuma wayoyin android sune wayoyin da jama’ suka fi amfani da su a wannan lokaci, tsarin free video call na whatsapp zai kasance a kan wadannan wayoyin da zarar an saki sabon version din. Sai dai kada mai amfani da wayar ya manta da cewar sai yayi “update” na whatsapp din nasa sannan zai sami damar more tsarin..

Akwai bukatar masu wayoyin iPhone da suyi “jail broken” din wayoyinsu kafin su sami damar amfana da sabon tsarin.

Ana sa ran akwai karin wasu sabbin abubuwan da za’a kara sanyawa a whatsapp nan gaba, abubuwan sun hada da voice mail, damar tura zip files ba tare da wani app ba da sauransu…

Kada ka mance wajen tura wannan labari zuwa abokanenka dake kan Facebook, twitter, whatsapp da sauransu