Share this on:
 • 34
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  34
  Shares

Jarumar kannywood Zainab Abdullahi wacce aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa yanzu ta dawo harkar film. Ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram kamar haka:

“Ina yiwa dukkannin masoyana albishir da cewa na dawo bakin aiki!! ALLAH ya bamu sa’a baki daya.”

Jarumar dai ta dauki lokaci mai tsawo batare da an ganta a film ba wanda sanadiyar haka ne ma wasu daga cikin yan kallon suka dunga muhawara a shafukan sada zumunta na magan ganu daban daban, wasu suce tayi rashin lafiya wasu kuma suce tayi aure ne.

Akwai lokacin da aka yi ta yada wani hoto nata dake nuna ta rame sosai wanda hakan ke nuni da alamar cewa tasha fama da rashin lafiya.

Akwai wadanda kuma suka yi ta yada jita-jitar cewa wai tayi accident har ma an yanke mata kafa, amma daga bisani jarumar ta fito ta karyata duk wadannan jita-jita da ake yadawa sannan ta kuma bayyana cewa ta na nan tana shirin dawo wa bakin aiki gadan gadan….


Share this on:
 • 34
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  34
  Shares