Mai girma shugaban kasar Najeria Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa na nan na iya bakin kokarin wajen ganin ta samarwa da matasa ayyukan yi da kudaden da suka kwato daga hannun jama’an da suka handame su a can baya.
shugaba-buhari

Sakatariyar ofishin ministan matasa wato Mrs Ololade Agboola ce ta karanta jawabin shugaban kasar yayin bikin karbar matasa masu yiwa kasa hidima(NYSC) kashi na farko a Gbakuta Iseyin can Jihar Oyo .

Buhari ya koka da yadda matsalar da ya gado ta rashin aikin yi ke kara ta’azzara wanda hakan ke kara dagula lissafin abubuwa a kasar baki daya, inda ya bayyana cewa sama wa matasa aikinyi shine babban abinda ke gaba gwamnatinsa..

Sannan ya kara da cewar suna nan suna kokarin shawo matsalar da ake fuskanta na matsalolin da matasan ke fuskanta a sansanoninsu da aka tura su. Matsala irinsu; rashin isashshen gurin zama, rashin isassun kudaden da za’a dauki nauyin su da sauransu.

Me kula da harkokin masu yiwa kasa hidima a jahar Oyo Mrs Funmilola Akin Moses ta bayyana cewa bana an turo musu matasa 1,692 wanda 732 daga cikinsu mazane sai kuma mata guda 960..