A jiya ne kungiyar masu tada kayar baya ta masu fafutukar nema wa yankin Niger-Delta yanci wato Niger-Delta avengers suka fitar da sanarwar cewa a shirye suke da su dakatar da hare-haren da suke kaddamar wa akan bututan man kasar nan.

Sanarwar dai ta fita ta shafin su na yanar gizo ta hannun mai magana da yawun kungiyar Mudoch Agbinibo inda ya sanar da cewa a shirye suke da su tattauna da gwamnati don samun maslaha.

Ya kara da cewar sun dauki wannan mataki ne don ganin cewa sojojin Nigeria na shirin yi ma yankin nasu kisan kare dangi wanda hakan zaifi shafar fararen hula.

“Mun fahimci cewa gwamnatin tarayya ta kirkiro wata sabuwar bataliya da aka yiwa lakabi da operation murmushin kada “Operation crocodile smile” wanda hakan ke gwada cewa zasu yi kisan kare dangi wa al’ummar yankin mu saboda dama abinda suka fi sha’awa kenan.”

ya kara da cewa suna kira ga Shugaban kasa da ya dauki salon mulki na irin kasashen da suka cigaba wajen barin kowa ya fito ya bayyana kokenshi ba tare da an dakatar dashi ba.

Mudoch din ya kara da cewar sun fa san ko menene ake kira da murmushin kada, domin ya samo asali ne daga “crocodile tears” wanda hakan ke nufin kisa ba daga kafa, saboda haka ba za’a yaudaresu da cewar wai ana atisaye ne kawai.

Idan aka samu zaman lafiya a yankin na Niger-Delta mai arzikin mai to za’a sami karuwar kudin shiga wa gwamnatin tarayya .

Shin jama’a kuna ganin anya ba tsoro suka ji ba ganin yadda sojoji suka yo hobbasa da niyyar murkushe su baki daya?