Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya ce babban burinsa shi ne ya kware wajen magana da harshen Turanci.
Zango, wanda aka haifa a garin Zangon Kataf na jihar Kaduna, ya yi karatun sakandare a birnin Jos na jihar Plateau ne.

Jarumin ya ce zai bar sana’arsa nan da dan wani lokaci domin ya je ya ci gaba da karatun boko.

A yanzu haka dai jarumin ya dauki malamin da yake ba shi darussa a gida, kafin ya koma makaranta don ci gaba da karatun.

“Yanzu haka na kammala sakandare kuma ina son ci gaba da karatu, ko da zuwa matakin difiloma ne. Abin da nake so shi ne na iya Turanci sosai,” in ji Adam Zango a wata hira da ya yi da BBC.

Sai dai wani abu da Adam ya ce yana ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu ‘yan boko suke masa kallon jahili duk kuwa da cewa “na yi karatun bokon sannan kuma ina da ilimin addini.”

Batun ilimin boko ne dai ya taba sa Adam ya wallafa wani habaici a shafinsa na Instagram da bai yi wa wasu ‘yan boko dadi ba, al’amarin da har ya sanya jarumin yin da-na-sani.