Shahararren maikudinnan kuma dan takarar neman shugabancin kasar amuruka wato Donald Trump ya bayanna cewa zasu koro duk wasu yan Nigeria zuwa gida idan yayi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Yayi wannan jawabi ne a yayin da yake yawon kampen inda ya bayyana cewa bakin haure musamman yan Nigeria da kuma yan mexico duk sunzo sun mamaye guraben ayyukan da ya kamata ace yan amerika ne ke aiki a gurin.

Domin dawo da martabar kasar amurka, to ya zama dole ne mu kori daukacin musulman dake kasar , yan mexico da kuma yan Africa musamman ma yan Nigeria.

Ya kara da cewa “sunzo sunyi kane-kane akan arzikin kasar mu, idan muka hana su sai su nemi su tada mana da hankali.” Inji Trump din.

Jama’a menene ra’ayinku akan hakan ?