-Advertisement-

JAMB Ta Fitar Da Tsarukan Bayar Da Admission Na Bana.

jamb-admission-processes

Hukumar Shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire wato Jamb ta fitar da irin tsarukan da zasu bi wajen baiwa dalibai admission na shiga guraben karatun a bana.

Wannan sanarwar dai an fitar da ita a shafin Jamb wanda ya biyo bayan wani meeting da sukayi da shugabannin malaman makarantun na kasa, inda suka yanke cewa za’a bi tsarin yawan point ne wajen bayar da admission wanda zata fara ne daga portal din jamb inda zasu tantance takardunsa kafin daga bisani mutum yaje makarantar da ya cike domin a kara tantance shi (screening.). Hakan dai ya biyo bayan soken jarabawar shiga jami’a(post ume) da makarantu kan shirya don tantance daliban da zasu dauka.

Hukumar Jamb din ta kara da cewar dole ne ya kasance Jamb ta baka admission na wucin gadi kafin ka sami damar zuwa screening din zuwa can makarantar da kake nema , inda sukayi alkawarin bude portal nan ba da jimawa ba.

Wadannan points dai za’a rabasu ne dangane da O’level da kuma sakamakon Jamb. Idan ya kasance mutum na amfani da result 1 ne misali WAEC ko NECO ko kuma GCE to zai kasance ya sami points goma (10 points). Har ila yau, wanda yayi amfani da result biyu(2 sittings) ya’alla ya hada waec da neco ne, ko kuma neco da gce to zai kasance ya samu points 2 ne kawai, saboda haka kenan wanda yayi amfani da one sitting zaifi samar samun admission cikin sauki.

Matakin tantancewa na gaba da hukumar tace ta tsara shine duk grade na jarabawa yana da maki, kamar A=6 points, B=4 points, C=3 points , to kaga kenan yanayin irin grades din da kake dasu to yanayin karfin damar da kake da ita wajen samun admission.

Haka zalika ma yawan marks na jamb da kaci shima yana da nashi points din, daga 180-200=20-23 points, 200-250=24-33 points, 251-300=34-43, 300-400=44-60 points. Bambancin shine point point 1 a duk mazaunin mark 5 na Jamb, kamar: 180-185=20, 186-190=21, da sauransu.

Hukumar Jamb din ta shaidawa manema labarai cewar kowacce makaranta na da alhakin zabar iya point da take bukatar mutum yakai kafin ya samu admission. Misali yanzu ace points da ake bukata ga mai son karantar likitanci(Medicine) yakai 90, sai ya kasance mutum bai kai wannan 90 points dinba to ba za’a bashi admission ba koda kuwa ace 280 ya ci a Jamb.

Jama’a me za kuce dangane da wannan tsari da ma’aikatar ilmi tazo dashi?

Ga mai bukatar karin bayani, sai a tuntube ni ta lambar wayata: 08135658217
Deen Dabai , arewamobile.com

5 Comments
 1. ABBAS says

  To mutanen suna zaton soke post ume wata alfarmace ashe ba’arabu da bukar ba kenan. Inajin gaskiya wannan zai hana wadanda suka chanchanta da yawa samun admission bana.

  1. Deendabai says

   wlh nima abinda nake gani kenan

 2. Babawo alfazazy says

  Tabdi deen wlh na lissafta point dina sai a hankali

  1. Deendabai says

   indai ya kai 50 ai ba case…

 3. Umarfaruqmaazu says

  To nida nake da 228 a jamb yaya kenan kuma inada olevel din lpai lau mlm deen

Comments are closed.