-Advertisement-

WAEC RESULT: Kaso 53 na dalibai sunci English da Math

Hukumar shirya jarabawar kamalla sakandire ta Waec ta fitar da sanarwa akan sakamakon jarabawa da aka gudanar a shekarar 2016. Sanarwar dake kunshe da bayanai kan yawan daliban da suka rubuta jarabawar zuwa ga adadin yawan wadanda suka ci.

A yayin da yake bayarda da bayanai wa manema labarai yau a Lagos, Shugaban hukumar Mr Olu Adenipekun ya bayyana cewar an samu cigaba sosai a sakamakon jarabawar bana duba da yadda abin yake a shekarun baya.

Mr Olu ya bayyana cewa dalibai 878,040 kimanin 53% ne suka sami Credit biyar ciki kuwa harda English da Math. Idan jama’a sukayi la’akari da shekarun baya to zasu ga cewa an samu gagarumin cigaba.

Shugaban ya kara da cewar mutane 1,552,758 ne suka rubuta jarabawar ta bana inda dalibai 1,014,573 (65.7%) suka sami akalla Credit 6.

Hukumar jarabawar tace ta rike sakamakon jarabawar dalibai 137,295 sabili da samunsu da akayi da laifin satar amsa yayin gudanar da jarabawar, inda yace suna nan suna bincike don tabbatar da laifin ko rashinsa…

Zaku iya duba sakamakon jarabawarku a shafin hukumar jarabawar ba wato www.waecdirect.org

ku kasance da arewamobile.com akoda yaushe don samun labarai gami da bayanai dangane da jarabawar.

Tura wannan labari zuwa abokanka dake Facebook , whatsapp , twitter dadai sauransu….

Comments are closed.